19 Afirilu 2022 - 19:48
Kungiyar Alshabab Ta Kai Hari A Majalisar Kasar Sumaliya

Majalisar Dokokin kasar Sumaliya ta fuskanci mummuna hari ne a daidai lokacin da sabbin yan majalsar dokokin kasa da aka zaba suke zaman sun a farko tun bayan da suka sha rantsuwar kama aiki, kuma kungiyar Alka’ida ta sanar da alhakin kai harin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun jikkata sai dai babu wani dan majalisa ko daya da ya ji ko kwarzane a lokacin kai harin , kuma lamarin ya faru ne adaidai lokacin day an majalisar suka fara tattaunawa kan lokacin da za’a zabi shugaban majalisar da sauran mukamai, da zai share hanyar zaben sabon shugaban kasar

A ranar Alhamis da ta gabata ce aka rantsar da sabiin yan majalisun dokokin kasar bayan zaben da aka gudanar fiye da shekara daya, wanda ayyukan tarzoma da rikicin neman shugabancin tsakanin shugaban mai ci dakuma kuma fira ministan kasar

Kungiyar ta Al shabab dake da alaka da kungiyar al’kaida dake haifar da tashin hankali da rashin zaman lafiya ya kasar ta sanar da alhakin kai mummunar kai harin

Ana ta bangaren dakarun samar da zaman lafiya tsa tsaro na Majalisar dinkin duniya UNSOM sun fitar da sanarwar yin Allah wadai da kai wannan mumman harin.

342/